Kasuwanci public
[search 0]
Mai Mult
Download the App!
show episodes
 
Shirin yakan duba yadda kasuwanci da tattalin arizikin kasashen duniya ke ciki. Kana yakan ji sabbin dubaru da hanyoyin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin 'Yan kasuwa da Masana’antu dangane da halin da suke ciki.
  continue reading
 
Loading …
show series
 
'Shirin Kasuwa A kai Miki Dole' na wannan makon tare da Ahmed Abba ya duba yadda harkokin kasuwanci ke tafiya a kasuwar dabbobi ta ƙasa da ƙasa da ke Maigatari ta Jihar Jigawa, wato kan iyakar Najeriya da Nijar, da kuma jin irin ƙalubalen da kasuwar ke fuskanta. Kasuwar ta Maigatari wadda ke iyakar Najeriya da Nijar na daya daga cikin manyan kasuwa…
  continue reading
 
Shirin Kasuwa Akai Miki Dole na wannan makon ya maida hankali ne kan hada-hadar kasuwaci tsakanin Najeriya da makwabciyarta Kamaru, da irin kalubalen da ƴan kasuwar Kamaru da diribobi daga ƙasashen biyu ke fadi tashi a kan iyakokin ƙasashen biyu. Ƴan kasuwar ƙasashen biyu na amfana da juna, a wasu manyan hanyoyin 10 da a hukumance aka san da su da …
  continue reading
 
Shirin 'Kasuwa A kai Miki Dole' na wannan makon tare da Ahmed Abba ya leka ne jihar Barno da ke arewa maso gabashin Najeriya, inda ya mayar da hankali kan tasarin tattalin arziki da ambaliyar baya-bayan nan ya haifarwa jihar da ma al'ummarta. Makonni biyu kenan tun bayan mummunar ambaliyar ruwa da ta afkawa wasu anguwannin birinin maiduguri na jiha…
  continue reading
 
Shirin kasuwa a kai miki dole tare da Ahmed Abba a wannan mako ya mayar da hankali kan matsi da tsadar rayuwa da kuma yadda wannan matsala ta jefa kaso mai yawa na magidantan Najeriya a halin tsaka mai wuya, matsalar da ke da nasaba da sabbin manufofin gwamnati ciki har da ƙarin farashin man fetur.De către RFI Hausa
  continue reading
 
Shirin "Kasuwa akai miki dole" tare da Ahmed Abba a wannan makon ya mayar da hankali ne kan matakin Babban Bankin Najeriya CBN na sayen motocin sulke na katsaita guda shida da ƙudin su ya haura naira biliyan 60, wanda gwamnan bankin da mataimakansa za su yi amfani da su, daidai lokacinda ƴan ƙasar ke fama da tsananin tsadar rayuwa. Ku latsa alamar …
  continue reading
 
Shirin kasuwa akai miki dole tare da Ahmed Abba a wannan mako ya waiwayi shirin gwamnatin Ghana na ban gishiri in baka manda a musayar zinare da man fetir, duk dai a ƙoƙarin da ƙasar ke yi na haɓaka tattalin arziƙinta. Tun a bara ne gwamnatin na Ghana ta ƙaddamar da tsarin na ban gishiri in baka manda, wanda ta ƙarbi tan dubu 40 na man disel da ƙud…
  continue reading
 
Shirin 'Kasuwa A kai Miki Dole' na wannan mako tare da Ahmed Abba ya duba yadda kasuwancin kifi a Najeriya ya ke neman ya gagari masu sana’ar saboda tsadar abincin da ake kiwon kifi da shi da farashin sa ya ƙaru, lamarin da ke barazana musamman ga ƙanana da matsakaitan ƴan kasuwa a fannin. Farashin buhun abincin kifi ya tashi daga N18,000 a shekara…
  continue reading
 
Shirin Kasuwa A kai miki Dole na wannan makon tare da Ahmad Abba ya tattauna irin asarar da aka yi a Najeriya sakamakon zanga zangar kwanaki 10 da ƴan ƙasar suka yi domin nuna adawa da tsadar rayuwa da rashin shugabanci na gari. Ministar masana’antu da Kasuwanci da kuma zuba jari na kasar Dr. Doris Uzoka Anite ta ce, alkakuma da suka tattara na wuc…
  continue reading
 
A yau shirin zai waiwai kasar Ghana, inda basusukan da ake bin kasar ya karu da dala biliyan 47.4 / Cidi biliyan 658.6 a cikin watanni biyun farko na shekarar 2024. Babban Bankin ƙasar ta Ghana ne ya fitar da wadandan alkaluma cikin wani rahoton da ya fitar na taƙaitaccen Bayanan Tattalin Arziki da Kuɗi na watan Mayun shekarar 2024. A cewar babban …
  continue reading
 
A wannan mako shirin ya mayar da hankali ne kan wani rahoto da hukumar ƙididigar ta Najeriya ta fitar cewa an sake samun hauhawan farashin kayayyaki wanda ƙasar ba ta taɓa gani ba cikin shekaru 30, daidai lokacin da gwamnatin ƙasar ke faɗi tashin kawowa al’umma sauƙi kan tsananin rayuwa da suke ciki, tare da amincewa da Naira dubu 70 a amatsayin ma…
  continue reading
 
Shirin 'Kasuwa Akai Miki Dole' a wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan sabon matakin gwamnatin Najeriya na sahale shigo da muhimman kayan abinci kamar su shinkafa da wake da alkama da masara ba tare da biyan ƙudin fito ba har tsawon watanni 5, domin rage tasirin tsaɗar kayan abinci da ƴan ƙasar ke fama da shi tun bayan ɗarewar …
  continue reading
 
Shirin 'Kasuwa akai Miki Dole na wannan makon ya maida hankali kan yadda gwamnatin Jamhuriyar Nijar, ta fara saidawa talaka shinkafa a farshi mai rahusa, domin saukakawa ƴan kasar radadin matsin tattalin da suke ciki sakamakon juyin mulki da sojoji suka yi. A ranar 26 ga watan Yunin da ya gabata gwamnatin Nijar ta hannun ma’aikatar kasuwanci ta kad…
  continue reading
 
Shirin 'Kasuwa akai Miki Dole na wannan makon ya maida hankali da kan kiranda wasu kungiyoyi suka yi wa gwamnatin Najeriya da ta yi wa Allah ta farfado da harkokin noma da sarrafa manja kamar yadda aka san ƙasar a baya. Kungiyar ɗalibai ta ƙasar ta yi kira ga shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya farfado da harkokin sarrafa manja da Allah ya wadata ƙasar…
  continue reading
 
Shirin zai maida hankali ne kan hahoton baya-bayan nan da Hukumar Kididdiga ta Najeriya ta fitar wanda ya bayyana yadda kasar ke ci gaba da fuskantar karin hauhawar farashin kayayyaki musamman na abinci, mafi muni da kasar ta gani a sama da shekaru 20. Rahoton wanda National Bureau of Statistic ta fitar a makon da ya gabata, ya cewa an fuskacin hau…
  continue reading
 
Shirin 'Kasuwa akai Miki Dole na wannan makon tare da Ahmad Abba ya maida hankali ne kan matakin gwamnatin Najeriya bukatar masu sana'ar POS da sauran masu mu'amala da na'urar da su garzawa hukumar rajistan kamfanoni ta kasar domin yin ragista kafin ranar 7 ga watan Yulin wannan shekara ta 2024.De către RFI Hausa
  continue reading
 
Shirin kasuwa akai miki dole tare da Ahmed Abba a wannan mako ya mayar da hankali kan matakin hukumar da ke yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annti EFCC na kaddamar na farautar tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello da kuma binciken wasu tsoffin mukarraban gwamnatin da ta shude kan cin hanci da rasha da kuma rufta da ci da dukiyar al’umma. A Najer…
  continue reading
 
Shirin Kasuwa A Kai Miki Dole a wannan makon ya maida hankali ne kan batun korafin ‘yan Najeriya ke yi game da rashin ganin sauyi a farashin kayan amfanin yau da kullum, bayan karyewar farashin ƙudaden ƙetare masamman dalar Amurka da sanadin tashin ta ne ya haddasa mummunan tashin farashin kayayyaki a kasar, wanda har hukumar ƙididdiga ta ƙasar ta …
  continue reading
 
Shirin Kasuwa a Kai Miki Dole a wannan makon ya maida hankali ne kan kananan sana’o’i da matasa ke yi don samun na abinci a lokacin azumin watan Ramadana a Damagaram da ke jamhuriyar Nijar. wasu daga cikin sana'oin da matasan sukafi mai da hankali akai dai sun hada da bredi ko kayan marmari ko kayan lambu da dai sauransu. Ku latsa alamar sauti don …
  continue reading
 
Shirin Kasuwa A Kai Miki Dole a wannan makon ya maida hankali ne kan rabon tallafin abincin naira biliyan 15, da Gidauniyar Aliko Dangote ta kaddamar a Najeriya. Wannan dai na daga cikin matakan rage radadin talauci a tsakanin al'ummar Najeriya, da gidauniyyar hamshakin attajirin Afirka ta kaddamar a birnin Kano da ke arewacin kasar. Ku latsa alama…
  continue reading
 
Shirin Kasuwa akai miki dole tare da Ahmed Abba a wannan makon ya yada zango ne a Tarayyar Najeriya, inda ya yi dubi kan matsanancin kuncin rayuwar da al’umman kasar suka shiga da har ta kai ana fasa rumbunan abinci ko tare manyan motocin dakon kaya a tituna ana kwasan abinci.De către RFI Hausa
  continue reading
 
A wannan makon shirin Kasuwa akai miki dole, zai yi duba ne game da bakar ukubar da al’ummar kasashen Nahiyar Africa ke fuskanta, a sanadiyar hauhawar farashin kayayyakin masarufi, musamman kasashen Nijeriya, Nijar da kuma Cameroon. Yanzu haka dai a iya cewa wannan yanayi na hauhawar farashin kayan masarufi tuni ya zame wa kasashen Nijeriya da Nija…
  continue reading
 
Loading …

Ghid rapid de referință